Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wasu mutane 15 da ake zargi da ayyukan batagari tare kuma da kwato motoci 20 da aka sace a sassa daban-daban na jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar SP Abdullahi Kiyawa ya fitar a Kano.
Ya ce kamawa tare da kwato motocin da aka sace ya samo asali ne bisa jajircewar rundunar don kawo karshen duk wasu laifuka a jihar.
Kiyawa ya ce, “Mun himmatu sosai wajen yakar satar motoci da duk wasu nau’ikan laifuka a fadin jihar Kano’’.
Kwamishinan ‘yan sanda, Muhammad Usaini Gumel, yayin da yake yaba wa jama’a bisa hadin kai da goyon baya da suke bayarwa, ya nanata kudurin rundunar na kawar da yyukan batagari.