Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana cewa yara 48 daga jihar sun ɓace sakamakon yawaitar satar yara da ake fama da ita a yankin.
Ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da rabon tallafin azumin Ramadan a ranar Juma’a a birnin Gombe.
Gwamnan bai bayyana takamaiman lokacin da aka sace yaran ba, amma ya nuna damuwa kan makomar su, yana mai cewa ba a san ko za a same su lafiya ba.
Ya kuma jaddada cewa duk da matakan tsaro da gwamnatin jihar ta ɗauka domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma, wasu na sukar waɗannan matakai duk da muhimmancinsu ga zaman lafiya.
Ya bayyana cewa tsaro alhaki ne na kowa da kowa, don haka akwai buƙatar jama’a su mara wa gwamnati baya wajen dakile duk wani abu da zai iya kawo barazana ga zaman lafiya da tsaron jihar.
A cewarsa, bayanan da ake da su sun nuna cewa yara 48 masu shekaru tsakanin biyu zuwa biyar an sace su daga jihar zuwa wasu sassa na duniya, yayin da iyayensu ke nan a cikin jihar.
Gwamnan ya kuma ce bayan sassauta dokar hana amfani da babura, an sace wani yaro a unguwar Orji Estate, amma an samu nasarar ceto shi.
Ya bukaci a dauki matakai masu tsauri domin tinkarar wadannan sabbin barazana tare da dawo da zaman lafiya a jihar, yana mai jaddada bukatar a sake nazarin halin da ake ciki domin daukar matakin da ya dace ko da kuwa yana da wahala.
Haka kuma, ya tunatar da yadda wasu da dokar hana sana’ar karafa ta shafa suka nemi taimakon shugabannin addini domin su sa baki a soke dokar, suna masu cewa ita ce hanyar samun abin rayuwarsu.
Gwamnan ya ce an dauki matakin ne domin inganta tsaro, dawo da zaman lafiya da kuma dakile yawaitar satar babura da sauran laifuffuka.
Ya kuma koka kan yadda ake lalata muhimman kayayyakin more rayuwa da suka hada da layin dogo da sauran kadarori masu daraja.
A cewarsa, har ma sabon filin masana’antu na Muhammadu Buhari da aka gina kan kudi Naira biliyan 26 bai tsira daga hannun masu barna ba, inda aka taba kayan lantarki da aka girka domin rarraba wutar lantarki daga madatsar ruwan Dadin Kowa zuwa filin.
Dangane da rabon tallafi, gwamnan ya ce an ware mutane 70,000 a fadin jihar domin cin gajiyar shirin.
Ya ce shirin ya mayar da hankali kan masu bukata ta musamman, kungiyoyin addini, gidajen marayu, kungiyoyin magoya bayan jam’iyya da sauran masu karamin karfi.
Ya kuma bukaci kwamitin rabon tallafin da su tabbatar da gaskiya, rikon amana da adalci, tare da raba kayan abinci kamar shinkafa, makaroni, taliya, mai da sukari cikin kwanaki uku. Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito wannan rahoto.













































