Tun bayan da aka koma mulkin dimokaradiyya a shekarar 1999, an yi yan majalisar dattijai shida a Sanatoriya Kano ta tsakiya, kuma ba tare da bayyana cewa daya daga cikin shidan ya yi fintinkau wajen tsayawa tsayin daka a tsakanin takwarorinsa ba, don kuwa kowa ya yi aikin Alkhairi na tsawon lokacin ba kuma don yana da gata ba, sai don kawai ya tabbatar da cewa ya kasance na musamman ta fuskar jarin dan Adam da ci gaban ababen more rayuwa tare da bayyana salon wakilci mai inganci a majalisar dokokin kasar.
Wannan hali na musamman ba kowa bane illa Sanata Basheer Garba Mohammed wanda aka fi sani da Basheer Lado, tsohon Dan majalisar dattijai mai wakiltar Kano ta tsakiya, kuma tsohon Darakta Janar na Hukumar yaki da Fataucin Bil Adama ta Kasa NAPTIP, kana tsohon Kwamishinan Tarayya a Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira, ta Kasa NCFRMI, sannan kuma tsohon memba na kwamitin yaki neman zaben shugaban Kasa a shekarar 2019, shi ne kuma Tsohon Mataimakin Darakta mai kula da shiyyar Arewa a kwamitin Tuntuba da Tattaunawa a karkashin Majalisar Yakin Neman zaben Shugaban kasa kuma mai ba da taimako na kowane lokaci ba tare da iyaka ba.
Kamar yadda aka ambata a baya lokacin da Nijeriya ta koma kan tafarkin dimokuradiyya a shekarar 1999, Kano ta tsakiya ta rabauta da Sanata Ibrahim Kura Muhammed, a matsayin Dan Majalisar Dattawa wanda ya yi mulki daga shekarar 1999 zuwa 2003, daga nan ne kuma Santoriyar ta samu Rufa’I Sani Hanga wanda ya yi mulki daga shekarar 2003 zuwa 2007, sannan Sanata Mohammed Adamu Bello, yazo kuma ya wakilci Santoriyar daga 2007 zuwa 2011.
Sai dai a shekarar 2011 zuwa 2015 Sanata Basheer Garba Muhammd ne ya kasance Dan Majalisar Dattawan mai wakiltar Kano ta Tsakiya, a lokacin Santiriyar ta samu albarka kuma hakika wadannan shekaru hudu, shekaru ne da al’ummar yankin ba za su taba mantawa da su ba, sai kuma Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da ya wakilci Santoriyar daga shekarar 2015 zuwa 2019 da kuma Sanata mai ci a yanzu Malam Ibrahim Shekarau.
Santoriyar Kano ta tsakiya ta shaida mafi kyawun lokacin da ta morewa da wakilci a tsakanin shekarar 2011 zuwa 2015 lokacin da Sanata Basheer Lado ya zama Sanata mai wakiltar shiyyar.
A lokacin ne zababben Sanata mai wakiltar mazabar da ta fi kowacce girma a Najeriya, ya samu nasarori sama da 108 na ayyukan mazabu da na tarayya.
Abin da ya fi daukar hankali shi ne ginin gadar Kundila, wadda aka fi sani da GADAR LADO, zai yi sha’awar kowa ya lura cewa, mutanen ne suka sanya wa wannan gadar suna, ba tare da jiran wani ko wata hukuma ta zabi sunan gadar ba, sai suka sanya mata suna.
Kazalika a likacin da Sanata Basheer Lado, yake wakilci nagari a majalisar dattawa, ya samu damar daidaita hanyar Kano zuwa Katsina wanda har yanzu ake ci gaba da gudanar da aikin a jihar.
Ayyukansa na bunkasa rayuwar al’umma daban-daban da ya gudanar a Santoriyarsa sun sanya mutane da yawa cikin farin ciki mara misaltuwa.
Watakilci na gari da irin rawar da ya taka lokacin da yake matsayin sanata sa kuma irin taimakon jama’a, a jihar Kano, yasa shugaban kasa Muhammadu Buhari bai bata lokaci ba wajen nada Sanata Lado a wani babban mukami mai matukar muhimmanci na kula da matsalar ‘yan gudun hijira a kasar nan.
An nada shi kwamishinan tarayya a hukumar kula da ‘Yan Gudun Hijira wadanda suka rasa Muhallansu, Kamar ko da yaushe Sanata Lado, bai bata lokaci ba wajen yin fintinkau a wajen gudanar da aikin sa a sabon nadin domin ya gudanar da shi cikin cancanta.
Ya yi sa’a ya kara da jerin nasarorin da wadda ta gabace shi Hajiya Sadiya Umar Farouq ta samu a matsayin minista.
Sanata Lado bai yi gaggawar neman yabo kan wasu ayyuka ba, amma ya samu cikin kankanin lokaci ya kafa wa kansa wani gagarumin tarihi a matsayinsa na shugaba mai kima da daraja wanda ya kasance kuma har yanzu, a hukumar kuma za a rika tunawa da shi a matsayin wanda ya zo ya gudanar da aikin sa kamar yadda ake tsammani.
Idan ba a manta ba, bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gamsu da nadin da aka yi masa a matsayin kwamishina na kasa, sai aka nada Sanata Lado a matsayin Darakta Janar na Hukumar Yaki da Fataucin Bil Adama ta Kasa NAPTIP da sauran mukamai da dama da suka ba shi damar bayar da gudumawa sosai a bangaren ci gaban Najeriya a matsayin kasa da kuma jam’iyyar sa ta APC.
A bayyane yake cewa mutanen Santoriyar Kano ta tsakiya na iya zama masu hikima wajen canza wakili, amma sun yi gaskiya domin Santoriyar ta na bukatar Mai ceto kamar Sanata Basheer Garba Lado, wanda zai ciro musu kitse daga wuta, kuma zai yi jagoranci na gari ba tare da nuna bambanci ba, wanda hakan bayyanannen abu ne da yake nuna shu din mutum ne na mutanensa.
Wadannan kadan ne daga cikin dalilai da suka sanya mutanen Santoriyar suke son ya dawo a matsayin Sanata a zaben shekara mai zuwa ta 2023.
Sun gani kuma sun shaida iyawarsa da jajurcewarsa, sun ji kuma sun ga tasirinsa, haka kuma sun lura da gibin da ke tattare da wakilcin sauran wakilai.
A wajensu Basheer Lado ne kawai amsar tambayarsu kuma sun bayyana cewa za su tabbatar da cewa ya yi nasara a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC da za a gudanar nan bada jimawa ba.
Wanda ya Rubuta: Mahmud wani kwararre kan harkokin yada labarai daga Kano.