A yau Litinin ne shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya isa jihar Kano ta filin jirgin sama na Malam Aminu Kano.

Da misalin karfe 11:00 na safe ne jirgin shugaban ƙasar ya sauka.

Solacebase ta ruwaito cewa, Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ne ya tarbi shugaba Buhari tare da ministocinsa da wasu manyan jami’an gwamnati.













































