
Gwamnatin jihar Kano ta umurci kwamishinan ‘yan sanda da ya fitar Sarkin Kano na 15, Aminu Bayero daga gudan sarki na Nasarawa.
Babban Lauyan Jihar kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar, Haruna Dederi yayin wani taron manema labarai ya bayyana cewa, tuni gwamnati ta kammala shirye-shiryen sake ginawa da kuma gyara kadarorin da suka hada da rushewa da sake gina katangar da ta lalace.
Ya ce, “Abin farin ciki ne, sanya hannu kan dokar da kuma mayar da mai martaba Sarki Muhammad Sunusi II an yi shi ne a ranar 23 ga Mayu 2024 kafin fitowar Dokar wucin gadi wacce kotu ta bayar.
“Bayan hukuncin da kotun ta yanke, gwamnatin jihar Kano ta umurci kwamishinan ‘yan sandan jihar da ya fitar tsohon sarki, saboda tuni gwamnati ta kammala shirye-shiryen sake ginawa da kuma gyara masarautar.
A dakace mu….