CBN ya cire sharadin takardar rantsuwar kotu wajen dawo da asusun bankin da ya daina aiki

Yemi Cardoso CBN Governor 750x430

Babban bankin kasa (CBN) ya cire wajabcin gabatar da takardar rantsuwar kotu ga kwastomomi da ke neman dawo da asusun bankinsu da ya daina aiki.

Hakan ya fito ne a cikin sabbin ƙa’idojin da aka sabunta kan yadda ake tafiyar da asusun banki marasa aiki, a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar 12 ga Maris, 2026, wadda aka aika wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi a faɗin ƙasar.

A cikin sanarwar da daraktan sashen manufofin kuɗi da ƙa’idoji na babban bankin, Rita Sike, ta sanya hannu, CBN ua bayyana cewa ya soke tanadin da ke sashe na 8.0(ii) da ke wajabta amfani da rantsuwar kotu wajen dawo da asusun banki marasa aiki, wanda a baya yake buƙatar kwastomomi su gabatar da rantsuwar kotu a matsayin wani ɓangare na tsarin dawo da asusun.

Babban bankin ya kuma fayyace cewa cire wannan sharadi ya shafi asusun banki marasa aiki ne kawai waɗanda har yanzu ba a tura su zuwa asusun haɗin kuɗaɗen da ba a karɓa ba.

Ya ƙara da cewa wannan sassauci bai shafi kuɗaɗen da tuni aka tura zuwa asusun haɗin kuɗaɗen da ba a karɓa ba ba.

A ƙarƙashin sabbin ƙa’idojin, yanzu bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi za su rika wallafa cikakkun bayanai na asusun banki marasa aiki da kuma kuɗaɗen da ba a karɓa ba.

CBN ya bayyana cewa wannan mataki ya biyo bayan shawarwari daga masu ruwa da tsaki, kuma wani ɓangare ne na ƙoƙarin sauƙaƙa hanyar samun damar amfani da kuɗaɗen da ke cikin asusun marasa aiki, tare da tabbatar da kariya ga ingancin tsarin kuɗi.

Sai dai ya bayyana cewa dole ne cibiyoyin kuɗi su ci gaba da amfani da tsauraran matakan tantancewa yayin da suke kula da buƙatun dawo da asusun banki marasa aiki.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here