Yanzu-yanzu; Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun hutun karamar sallah

Minister of Interior Dr. Olubunmi Tunji Ojo

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Alhamis 19 ga Maris da kuma Juma’a 20 ga Maris, 2026 a matsayin ranakun hutun a fadin ƙasa domin bikin Eid-el-Fitr, wanda ke nuna ƙarshen watan azumin Ramadan na Musulmi.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya.

A cikin wata sanarwa da babbar sakatariyar ta ma’aikatar, Magdalene Ajani, ta fitar a ranar Talata, ministan ya taya al’ummar Musulmi murna tare da taya Musulmi farin ciki kan nasarar kammala azumin watan Ramadan.

Ya buƙaci Musulmi da su ci gaba da riƙe darussan soyayya, karamci, zaman lafiya, haƙuri da sadaukarwa da aka koyar a lokacin watan azumi.

Ya kuma nuna a muhimmancin ci gaba da waɗannan halaye domin inganta zaman tare cikin lumana a tsakanin al’umma.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here