Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya baiwa Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) umarnin da ta bude asusun bankin Gwamnatin Jihar Osun nan take ta hanyar komawa kotu domin soke umarnin kulle asusun, inda ya bayyana cewa matakin na iya shafar amincewar jama’a kafin zaben gwamnan jihar da za a yi a ranar 15 ga watan Agusta.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, Shugaban ya ce ya abin kunya ne daukar EFCC ta dauki wannan mataki duba da lokacin ta neman umarnin kotu na kulle asusun jihar. Amma duk da haka ya ce ba ya kalubalantar ikon hukumar ko ‘yancinta.
“Na samu labarin cewa Hukumar EFCC ta samu umarnin kotu a ranar 5 ga watan Agusta, 2026, don kulle asusun Gwamnatin Jihar Osun. Dole ne in bayyana cewa na ji kunya matuka, ba saboda EFCC ta aiwatar da aikinta bisa umarnin kotu ba, sai dai saboda lokacin da hukumar ta zaba wajen aiwatar da wannan mataki,” in ji Tinubu.
Shugaban ya bayyana cewa matakan da hukumomin gwamnatin tarayya ke dauka ana danganta su da Shugaban Kasa, ko da yake ba a sanar da shi kafin a dauki irin wadannan matakai ba.
Tinubu ya ce tun bayan hauwa mulki, ya rika barin EFCC da sauran hukumomin tsaro su gudanar da ayyukansu ba tare da tsoma baki ba.
“Tun bayan da na hau mulki, na rika bayyana wa akai-akai cewa dole ne a bar hukumomin yaki da cin hanci da lamarin doka su gudanar da ayyukan da doka ta ba su bisa cikin ‘yanci, kwarewa, ba tare da tsoro ko son kai, ko tsoma bakin ba,” in ji shi.
Shugaban ya kara da cewa duk da yake yana goyon bayan ‘yancin hukumomin yaki da cin hanci, amma yanayin da ke Jihar Osun ya tilasta masa shiga tsakani saboda jihar na shirin gudanar da zaben gwamna.
Tinubu ya baiwa EFCC umarnin ta koma kotu ta janye umarnin kulle asusun Gwamnatin Jihar Osun.
“Saboda haka, na baiwa EFCC umarnin ta tafi kotu nan take ta soke umarnin kuma ta dakatar da duk wani mataki da ta dauka kan Gwamnatin Jihar Osun dangane da wannan lamari,” in ji Shugaban.
Wannan umarni na zuwa ne bayan cece-kuce da aka yi kan kulle asusun Gwamnatin Jihar Osun, inda ‘Yan adawa, lauyoyi da kungiyoyin farar hula suke bayyana damuwa cewa matakin na iya shafar gwamnati da kuma tayar da tambayoyi kan tsoma baki daga bangaren siyasa kafin zaben gwamna.












































