Gwamnatin Jihar Kano ta dakatar da dukkan ayyuka a karkashin shirin riga kafin cutar zazzabin cizon sauro na lokaci-lokaci (SMC) a fadin jihar kuma ta kafa kwamitin bincike domin gano yadda aka aiwatar da shirin.
An sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano, Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa, ya fitar a ranar Alhamis, inda ya ce matakin na da nufin tabbatar da gaskiya, rikon amana da tsafta wajen aiwatar da wannan shirin na ceto rayukan al-umma.
A cewar sanarwar, dakatarwar ta fara aiki nan take bayan kafa kwamitin bincike da aka baiwa umarnin ya bibiya tare da gano yadda aka shirya, rarraba da aiwatar da shirin SMC a Jihar.
Ma’aikatar ta ce binciken zai shafi ayyukan shirin, takardu, bayanan ma’aikata da duk sauran ayyuka.
“A matsayin wani bangare na kudurin kwamitin, an dakatar da dukkan ayyukan da ake yi na badawa, rarrabawa da hulda da al’umma a karkashin shirin SMC har sai an kammala binciken,” in ji sanarwar.
Haka kuma an dakatar da Manajan Shirin nan take, inda aka mika nauyin shirin ga babban jami’in da ke bin shi domin tabbatar daidaito a lokacin binciken.
Gwamnatin ta bayyana cewa an kafa kwamitin ne don tabbatar da gaskiya, adalci da kwarewa a binciken.
SolaceBase ta rawaito ce kwamitin na karkashin jagorancin Darakta Janar na Hukumar Yaki da Cutar mai karya garkuwa ta Jihar Kano (SACA) Dr. Usman Bashir.
Sauran mambobin su ne Darakta Janar na Hukumar Kula da Lafiya Matakin Farko ta Jihar, Prof. Salisu Ahmad Ibrahim, Darakta Janar na Hukumar Magani da Kayan Aikin Lafiya, Pharm. Ghali Sule, Sakataren Zartarwa na Hukumar Kula da Asibitoci, Dr. Mansur Mudi Nagoda, Darakta Janar na Cibiyar Kula da Cututtuka ta Kano, Prof. Muhammad A. Abbas, Sakataren Zartarwa na Asusun Lafiya na Kano, Dr. Fatima Usman Zahradden, Sakataren Zartarwa na Hukumar Inshorar Lafiya ta Jihar Kano, Dr. Rahila A. Mukhtar da Mai Rikon Mukamin Darakta Janar na Hukumar Kula da Asibitocin Masu Zaman Kansu, Khadijah Hussein Said.
Darakta na Gudanarwa da Ayyukan Jama’a a Ma’aikatar Lafiya, Nazeer Tanko Kyaure, zai zama sakataren kwamitin.
Bugu da kari, Ma’aikatar ta umurci Jami’in Kulawa da shirin, abokan aikinsa da sauran masu ruwa da tsaki da su je ofishin ta tare da dukkan takardun shirin da suka dace, ciki har da takardar amincewa da tsari, bayanan rarrabawa da jerin sunayen mutanen da aka shirin tantance a shirin.
Sanarwar ta ce gwamnati zata ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da gaskiya, rikon amana da amfani da dukiyar jama’a yadda ya dace a dukkan shirye-shiryen lafiya.
“Binciken da ake yi na da nufin karfafa yadda ake gudanar da shirin da kuma tabbatar da cewa ayyukan lafiya sun ci gaba da amfanar da al’ummar Jihar Kano yadda ya kamata,” in ji ta.
Gwamnatin ta kuma tabbatar wa abokan aiki da jama’a cewa binciken na da nufin inganta yadda ake aiki ba don kawo cikas ga kokarin yaki da zazzabin cizon sauro ba.
Ta yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su ba da cikakken hadin kai ga kwamitin binciken da kuma ci gaba da jajircewa wajen tallafawa kokarin inganta samar da kiwon lafiya a fadin jihar.
“Muna kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su ba da cikakken hadin kai ga kwamitin binciken da kuma ci gaba da jajircewa wajen tallafawa kokarin da aka yi niyya na inganta samar da kiwon lafiya a fadin Jihar,” in ji sanarwar.















































