Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Jihar Kano (KNCDC), a ranar Laraba ta bayyana cewa ta fara bincike kan rahoton mutuwar yara fiye da hamsin a Karamar Hukumar Rano, biyo bayan zargin bullar cutar sankarau.
Darakta Janar na hukumar KNCDC, Farfesa Muhammad Abbas, ne ya bayyana haka yayin taron manema labarai a hedkwatar hukumar da ke Kano, sakamakon damuwar da Majalisar Dokokin Jihar Kano ta nuna kan mace-macen da aka rawaito.
Ya ce hukumar ta tattara alkaluman mazauna Karamar Hukumar ta Kano, mutum 32 da suka kamu da cutar a wannan shekarar, inda aka samu mutum 25 daga cikinsu a watan Agusta, shida a watan Yuli sai guda daya a watan Mayu.
“Bakwai daga cikin marasa lafiya 32 an kwantar da su ne a Asibitin Cututtuka Masu Yaduwa (IDH), wanda shi ne cibiyar da aka ware don killacewa da jiyyar masu cutar sankarau a Kano.”
Abbas ya ce binciken gano marasa lafiya da aka gudanar a ranar 19 ga watan Agusta, biyo bayan rahoton samun mutum hudu a ranar 13 ga watan Agusta, ya kai ga gano karin mutum goma da suka kamu da cutar da mace-mace guda biyu.
Ya danganta banbancin da ke tsakanin alkaluman da aka tabbatar a hukumance da kuma rahoton mutuwar yara fiye da hamsin da jinkirin kai rahoto asibiti, inda wasu marasa lafiyar ke karbar magani a gida ko kuma wurin masu maganin gargajiya maimakon neman kulawar likitoci.
Ya bayyana cewa KNCDC na gudanar da binciken gano musabbabin mutuwa ta hanyar tattaunawa da dangin wasu daga cikin mamatan, domin tantance yanayin da ya fito da ajalinsu da kuma tabbatar da ko cutar sankarau ce ta yi sanadi ko kuma wata jirar daban.
Darakta Janar din ya yi kira ga iyaye da masu rainon yara da su gaggauta kai yaran da ke nuna alamun cutar sankarau zuwa cibiyoyin kiwon lafiya, yana mai gargadin cewa jinkirta kai su asibiti na iya kaiwa ga mummunan kalubale ko mutuwa.
Abbas ya bayyana cewa Jihar Kano ta yi rajistar mutum fiye da dubu talatin da takwas da ake zargin sun kamu da cutar sankarau tun lokacin da ta bulla a shekarar 2022, inda aka tabbatar da fiye da dubu talatin da daya daga baya.
Ya ce fiye da kashi hamsin da biyar na wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar yara ne da ba su taba karba allurar riga-kafi ko sau daya ba, yayin da kashi 16 cikin dari kuma suka karbi riga-kafin amma ba duka ba, inda ya jaddada bukatar tsananta riga-kafi a fadin jihar.
Ya jinjina wa Gwamnatin Jihar Kano da Majalisar Dokoki bisa goyon bayan da suke bayarwa, sannan ya yi kira ga mazauna jihar da su gaggauta kai rahoton cututtuka masu yaduwa zuwa cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko, na biyu ko na uku domin sauwaka daukar mataki da wuri da kuma hana asarar rayuka nan gaba.














































