Shahararren jarumin Nollywood Taiwo Hassan ‘Ogogo’ ya rasu

Taiwo Hassan ‘Ogogo

Shahararren jarumin Nollywood, Taiwo Hassan, wanda aka fi sani da Ogogo, ya rasu.

‘Yar jarumin, Kira Taiwo ce ta sanar da mutuwarsa a yammacin ranar Lahadi a wani sako na kai tsaye da ta yi a shafinta na Instagram.

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan Kira ta bayyana cewa mahaifinta yana fama da cutar kansa ta mataki na hudu.

Taiwo Hassan ya kasance wani babban jigo a masana’antar shirya fina-finan Najeriya, musamman an san shi da rawar da yake takawa a fina-finan Yarbanci da kuma gudunmawar da ya bayar wajen bunkasa Nollywood.

Kafin rasuwarsa, an ruwaito an yi kokarin nemo masa magani a asibiti.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here