Masarautar Kano ta gabatar da kudurin gwajin shan kwayoyi ga masu neman sarauta

Kano Emirate

Masarautar Kano ta amince da gudanar da gwajin ta’ammali da miyagun kwayoyi a matsayin wani mataki na samun sarauta ga masu son mukami a masarautar.

Hakimin Dambatta, Dr. Mansur Adnan, ne ya bayyana hakan a ranar Asabar yayin wani taron fadakarwa game da illolin safara da shan miyagun kwayoyi da aka gudanar a fadar sa da ke Dambatta.

Ya bayyana cewa daukar wannan matakin ya zama dole saboda mummunar illar da shaye-shayen kwayoyi ke da shi ga daidaikun mutane da ma al’umma baki daya.

Adnan ya kara da cewa, wadannan illolin na shaye-shaye ne suka sanya Masarautar Kano ta bukaci lallai masu neman mukamin sarautun gargajiya su yi gwajin kwayoyi kafin a ba su sarauta.
Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya ruwaito cewa, gangamin ya tara daukacin sarakunan shiyya-shiyya da na mazabu na karamar hukumar Dambatta domin wayar musu da kai kan illolin fataucin miyagun kwayoyi da shaye-shaye.

Kwamandan Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) na shiyyar Dambatta, Zailani Muhammad, ya ce babban burin hukumar shi ne yaki da fataucin kwayoyi da shaye-shayensu domin kare rayuka da makomar al’umma.

Muhammad ya bukaci shugabannin gargajiya da mazauna yankin da su ba hukumar hadin kai ta hanyar kai rahoton dillalan kwayoyi da kuma wuraren da matasa ke siyarwa ko amfani da miyagun kwayoyin.

Ya ce hukumar a shirye take a kowane lokaci don karbar rahotanni, shawarwari da korafe-korafen da suka shafi yaki da shaye-shaye da fataucin miyagun kwayoyi.

Kwamandan ya jaddada cewa nasara a yakin da ake yi da shaye-shaye da fataucin kwayoyi na bukatar hadin gwiwar gwamnati, sarakunan gargajiya, iyaye, malamai da sauran gaba dayan al’umma.

Haka kuma, Muhammad ya ja hankalin mahalarta taron kan illolin shaye-shayen kwayoyi; abubuwan da ke janyo matasa shiga harkar kwayoyi da kuma alamomin da ya kamata iyaye su rika lura da su ga yayansu.

Ya nuna wasu daga cikin kwayoyin da matasa suka fi yawan amfani da su tare da bayyana haduransu.

A nasa bangaren, Babban Jami’in ‘Yansanda na Shiyyar Dambatta (DPO), SP Ibrahim Kwasarawa, ya bayyana cewa akasarin laifukan da matasa suke al’umma suna da alaka da shaye-shayen kwayoyi.

Daga karshe, Kwasarawa ya yi kira ga iyaye da su rika sanya ido a kan ‘ya’yansu tare da yi musu jagoranci na gari zuwa ga dabi’u masu kyau.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here