Shugaban kasa Bola Tinubu ya rattaba hannu kan kasafin bana

TINUBU KASAFI
TINUBU KASAFI

Shugaba kasa Bola Tinubu ya rattaba hannu kan kasafin bana, domin ya zama doka a alkawurran da ya dauka na tabbatar da tsarin kasafin kudi, wanda ake iya tsinkaya, da inganci.

Tinubu ya amince da kudirin ne a gidan gwamnati, a ranar Litinin, jim kadan bayan ya dawo Abuja daga Legas.

Da yake jawabi yayin rattaba hannu kan kudirin dokar, ya tabbatarwa da ‘yan kasa cewa za’a bi diddigin aiwatar da kasafin kudin ne yadda ya kamata, tare da sanya ido sosai a kai.

Shettima ya kaddamar da sabon Ofishin Gwamnan Kano da aka sake wa fasali

Shugaban ya kara da cewa: “Dukkan hanyoyin da hukumomi za su bi domin tabbatar da aiwatar da su cikin himma”.

“An umurci dukkan MDAs da su dauki nauyi tare da bayar da rahoton ayyukan kasafin kudi na wata-wata ga ma’aikatar kasafin kudi da tsare-tsare na tattalin arziki, wanda hakan zai tabbatar da sahihancin hakan.

Ministan Kudi da Hadin Kan Harkokin Tattalin Arziƙi zai rinka yin bita akai-akai tare da ƙungiyar gudanar da tattalin arziƙi, baya ga haka, zan jagoranci tarukan majalisar gudanar da Tattalin Arziƙi na lokaci-lokaci,” in ji shi.

Uwargidan shugaban kasa ta ziyarci jaririn farko na shekarar 2024 a Abuja

Manyan batutuwa da kasafin kudin banan na Naira Tiriliyan 28.7 da suka ba da fifiko sun hada da samar da tsaro da na cikin gida, samar da ayyukan yi, inganta tattalin arzikin kasa, inganta zuba jari, bunkasa jari, rage talauci, da samar da zaman lafiya.

Shugaba Tinubu ya jaddada cewa kudurinsa na inganta harkokin zuba jari, tare da samar da al’umma masu bin doka da oda, ya fara ne da muhimman gyare-gyare a bangaren shari’a na kasar nan, wanda aka kama kudade a cikin dokar kasafin shekarar nan da mu ke ciki.

“Bayar da kudade ga bangaren shari’a babban bangare ne a kokarinmu na tallafa wa al’umma mai adalci da bin ka’ida. An kara wa bangaren shari’a kudin hannun doka daga naira biliyan 165 zuwa naira biliyan 342,” A cewar Tinubu.

Wasu daga cikin muhimman alkaluma sun hada da kashe kudi na naira tiriliyan 10, kashe kudi akai-akai na Naira tiriliyan 8.8, biyan basussuka na naira tiriliyan 8.2, da canja wurin doka na Naira tiriliyan 1.7.

Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, sun halarci rattaba hannun.

Sauran manyan jami’an gwamnati da suka halarci takaitaccen bikin sun hada da: Ministan kudi da hadin kan ma’aikatar tattalin arziki Wale Edun, da Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, hadi da Ministan kasafin Kudi da tsarin tattalin Arziki Sanata Atiku Bagudu, da mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here