Kasafin Kudin 2024: Tinubu ya umarci hukumomi da ma’aikatu su rinka bada rahoton wata-wata

President Bola Tinubu
President Bola Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya sanya hannu kan kasafin kudin shekarar 2024 domin ya zama doka da nufin cika alkawurran da ya dauka na tabbatar da tsarin kasafin kudi akan lokaci.

Tinubu ya amince da kudirin ne a fadar shugaban kasa dake Abuja ranar Litinin, jim kadan bayan ya dawo daga Legas.

Karanta wannan: Shugaban kasa Bola Tinubu ya rattaba hannu kan kasafin bana

Da yake jawabi yayin sanya hannun, shugaban ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa za a aiwatar da kasafin yadda ya kamata tare da sanya ido sosai a kai.

Manyan batutuwan da kasafin kudin 2024 na Naira Tiriliyan 28 da biliyan 7 suka ba da fifiko sun hada da tsaro da samar da ayyukan yi da inganta tattalin arziki sai farfado da hanyoyin zuba jari da sauran su.

Karanta wannan: 2024: Mun kara samun damar daukar matakan da za su kai mu gaci-Walin Kazaure  

Shugaban ya jaddada cewa kudurinsa na inganta harkokin zuba jari ya fara ne da muhimman gyare-gyare a bangaren shari’a.

A kiyasin da aka yi ga wasu muhimman bangarori na kasafin, Manyan ayyuka za’a kashe kudi naira tiriliyan 10, ayyukan yau da kullum Naira tiriliyan 8 da biliyan 8, hidimar bashi an ware Naira Tiriliyan 8 da biliyan 2, sannan kuma bisa doka ya tura Naira Tiriliyan 1 da biyaln 7.

Shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio da kakakin majalisar wakilai Tajudeen Abbas sun halarci rattaba hannun.

Sauran manyan jami’an gwamnati da suka halarci bikin sun hada da ministan kudi Wale Edun, Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, Ministan Kasafin Kudi da tsaren tattalin arziki, Sanata Atiku Bagudu, da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here