Yan-sanda suna bincike akan sace shugaban karamar hukuma a Nasarawa

'yan sanda, jami'i, zargin, kisan kai, neman, Anambra
Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta sanar da kama jami'inta, Insfekta Audu Omadefu mai lamba (AP No.362178) da laifin kisan kai. DSP Tochukwu Ikenga...

Rundunar yan-sanda a jihar Nasarawa tace tana ci gaba da gudanar da bincike kan sace shugaban karamar hukumar Akwanga Safiyanu Isa-andaha, da yan bindiga suka yi.

Mai Magana da yawun rundunar yan sandan jihar DSP Ramhan Nansel, ne ya tabbatar da hakan ganema labarai ranar Talata a Lafiya babban birnin jihar.

Karanta wannan: Kasafin Kudin 2024: Tinubu ya umarci hukumomi da ma’aikatu su rinka bada rahoton wata-wata

Ramhan yace kwamishinan yan sandan jihar Umar Nadada, ya bada umarnin cewa jami’an ‘yan sandan su bazama neman ‘yan bindigar tare da kubutar da shugabn karamar hukumar da wani mutum guda da aka sace su tare.

Yace tun da fari sun sami bayanai cewa an sace shugaban karamar hukumar ne da wani mutum guda a kauyen Ningo cikin karamar hukumar Akwanga da misalin karfe 8 da minti 30 na dare.

Ya kuma bukaci al’ummar yankunan da su bada bayanan da za su taimaka wajen kubutar da wadanda aka sace, tare da kama yan ta’addar.

Karanta wannan: Shugaban kasa Bola Tinubu ya rattaba hannu kan kasafin bana

Kazalika mashawarci na musamman ga gwamanan jihar Nasarawa akan harkokin masarautu Haruna Kassimu, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Yace shugaban karamar hukumar da wani mai suna Adamu Custom an yi awon gaba da su ne a kauyen Ningo na karamar hukumar Akwanga da misalign karfe 8:30 na daren Litinin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here