Gwamnatin tarayya ta dauki matakin soke tantance shaidar karatun digiri daga jami’o’in kasashen Benin da na Togo.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Augustina Obilor-Duru, ya fitar a madadin Daraktan yada labarai na ma’aikatar ilimi ta tarayya.
Karanta wannan: Yan-sanda suna bincike akan sace shugaban karamar hukuma a Nasarawa
Dakatarwar ta biyo bayan wani rahoton binciken kwa-kwaf da jaridar Daily Nigerian ta gabatar mai take “Yadda wakilin jaridar DAILY NIGERIAN ya samu digirin daga Cotonou a cikin sati 6”.
Karanta wannan: Jarumin fina-finan Nollywood, Zack Orji yana jinya
Sanarwar ta ce yanzu haka za’a ci gaba da jiran sakamakon bincike daga ma’aikatun harkokin waje da ilimi na kasar nan da kuma na kasashen biyu har ma da hukumar tsaron farin kaya DSS, da kuma hukumar kula da masu yi wa kasa hidima.
Karanta wannan: Bayan rahoton da Jaridar Solacebase ta yi an gyara wani asibiti a Jigawa
Ta kara da cewa ma’aikatar ilimi ta tarayya na yi wa al’ummar kasar nan barka da sabuwar shekarar miladiyya ta 2024.