Aƙalla mutum 20 sun mutu a rikicin ƙabilanci a Taraba

4de17ab0 f2d2 11ed ac65 d54f5c262321
4de17ab0 f2d2 11ed ac65 d54f5c262321

Aƙalla mutum ashirin ne suka mutu sakamakon wani rikicin ƙabilanci da ya ɓarke tsakanin ƙabilun Wurkunawa da kuma Karimjo a ƙaramar Hukumar Karim Lamido ta jihar Taraba.

An kuma ƙona gidaje da dama da asarar dukiya mai dimbin yawa.

Tashin hankalin ya samo asali ne kan batun sarautar gargajiya a yankin.

A cikin makon da ya gabata ne gwamnan jihar ta Taraba Darius Ishaku ya bai wa Alhaji Yakubu Abubakar Haruna sanda a matsayin sabon sarki a masarautar Wurkum da ke Karamar Hukumar Karim Lamido a jihar Taraba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here