Kara tabarbarewar tsaro a Najeriya abu ne mai ban tsoro – Umma Getso

IMG 20220207 WA0001
IMG 20220207 WA0001

Tsohuwar ‘yar takarar mataimakiyar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Young Progressive Party, YPP Hajia Umma Abdullahi Getso, ta bayyana takaici dangane karuwar barazanar tsaro a fadin kasar nan.

A wata hira ta musamman da ta yi da Solacebase, a Abuja, Hajiya Umma Getso ta ce gwamnatin tarayya ba ta da ingantattun kayan aikin da za ta magance matsalar rashin tsaro da ke addabar kasar.

Hajiya Getso ta bukaci matasa da su guji tashin hankali da siyasar kudi domin wadannan suna da mummunan tasiri ga ci gaban kasa.

“Jam’iyyar mu ta Young Progressive Party ta bazu a cikin shiyyoyin siyasar kasar nan guda 6 tare da kokarin sauya tsarin rayuwar matasa a matsayin jagororin gobe, ta yadda za Su taimaka wajen kawo ci gaba.

Da take magana kan kokarin da gwamnatin tarayya ke yi a halin yanzu na dakile matsalar tsaro, Umma Getso ta ci gaba da cewa kamata ya yi gwamnati ta dauki matakan gaggawa kawo karshen matsalar.

“A bayyane yake cewa yawancin al’ummomi a Katsina, Sokoto, Zamfara da Neja ba a zaune lafiya suke ba, saboda hare-haren ‘yan ta’adda, wanda hakan ya sanya da dama suka zama ‘yan gudun hijira.

Getso ta bukaci ‘yan Najeriya kada su bari masu siyan kuri’u su rinjaye su da kudi a yayin zaben shekarar 2023 mai zuwa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here