Kimanin mutane 23 ne suka rasa ransu bayan da wasu gungun yan ta’adda suka kai hari kauyen unguwar Danko dake yankin Kakangi na karamar hukumar Birnin Gwari dake jihar Kaduna.
Yan ta’addan wadanda suka shiga kauyen a daren ranar alhamis, sun yi harbe harbe, daga bisani suka yi garkuwa da wasu mazauna yankin. .
Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Kakangi a majalisar dokokin jihar Yahya Musa Dan Salio ne ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce yan ta’addan sun kashe sama da mutane 23 yayin da mutane 5 suka jikkata, inda wasu daga cikin mutanen yankin suka bazama dazuka.
Shima Sakataren shugaban karamar hukumar ta Birin Gwari Alhassan Ibrahim Saulawa ya tabbatar da jikkatar mutane sama da 20.
Har kawo yanzu dai ,ba’a san iya adadin mutanen da aka yi garkuwa dasu ba da wadanda suka bace a cikin daji, sai dai mai Magana da yawun rundunr yan sanda ASP Mansur Hassan yayi alkawari fadada bincike domin gano gaskiyar abinda ya faru.