Rundunar ‘yan sanda a Abuja ta ce, an tsinci gawar marigayi tsohon shugaban hukumar kula da shige da fice NIS David Shikfu Paradang, a kujera a dakinsa na otal bayan ya karbi bakuncin wata mata.
Rundunar ta ce, wannan ya biyo saɓanin rahotannin da ake yadawa na cewa wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka kashe shi.
Sanarwar da SP Josephine Adeh, mai magana da yawun rundunar yan sanda ya fitar, mai taken “Yan sandan FCT sun mayar da martani kan mutuwar Kwanturola Janar David Parradang mai ritaya” ya ce Parradang dai ya gamu da ajali ne kwana guda bayan da ya je otal din da wani abokins ya gayyace shi wanda jami’in soja ne, har ma ya samu rakiyar ma’aikatan otal din.
Ya kara da cewa, “Bisa rahotannin baya-bayan nan na zargin cewa an yi garkuwa da tsohon Kwanturola Janar na hukumar kula da shige da fice ta Najeriya, David Shikfu Parradang mai ritaya, daga bisani kuma aka kashe shi, muna so mu fayyace gaskiyar lamarin da ya faru domin ganin an yada sahihancin bayanai ga jama’a.
Labari mai alaƙa: Yan bindiga sun kashe tsohon shugaban hukumar kula da shige da fice Parradang
“A ranar 3 ga Maris, 2025, da misalin karfe 12 na dare Mr. Parradang ya isa otal din Joy House da ke Unguwar 3 Junction, yana tuka wata bakar mota kirar Mercedes Benz.
“Ya shiga otal din, ya biya kudi naira dubu ashirin da biyu (N22,000) na kwana daya.
“Ba da jimawa ba, sai ya umurci ma’aikaciyar dakin otal da ta raka wata bakuwa mace da ta zo dakinsa, to amma wannan matar ta bar harabar otal din da misalin karfe 4 na yammacin wannan rana kuma Parradang bai fita daga dakinsa ba bayan da matar ta tafi”.
“Da misalin karfe 4:00 na safe ranar 4 ga Maris, 2025, wani abokinsa wanda jami’in soja ne, wanda ya damu da lafiyarsa, ya gano shi zuwa otal.
“Bayan isowar, mai karbar bakuncin otal din da jami’in ya zarce zuwa dakinsa, inda aka iske Parradang ya mutu, a zaune a kan kujera.
“An sanar da ofishin ‘yan sanda kuma jami’ansu suka isa wurin da lamarin ya faru ba tare da bata lokaci ba, suka tsare wurin, suka dauki hotuna, tare da tattara duk wasu shaidun da suka dace don kare mutuncin wurin da lamarin ya faru.
“An mika gawar zuwa Asibitin kasa domin gudanar da ayyukan da suka dace, inda zuwa yanzu haka ma’aikatan Otal din suna bayar da hadin kai ga binciken ‘yan sanda, inda ake kokarin ganin an kamo matar.