ACF ta dakatar da Shugaban Kwamitin Amintattu, ta yi umarnin a yi binciken kudi

Dalhatu 750x430

Kwamitin Zartarwa na Kasa (NEC) na Kungiyar Tuntubar ta Arewa (ACF) ya dakatar da Shugaban kwamitin amintattu (BOT), Alhaji Bashir Dalhatu, bisa zargin almundahana da rashin iya gudanarwa, ta kuma umarci a gudanar da cikakken bincike kan kudin kungiyar.

Kungiyar ta yanke shawarar ne biyo bayan wani taron gaggawa na kwamitin zartarwa na kasa da aka gudanar a Kaduna a ranar Laraba, a cewar Sakataren Yada Labarai ACF din na Kasa, Farfesa Tukur Mohammed Baba.

Baba, wanda ya shaida wa manema labarai jim kadan bayan taron, ya ce NEC ta kuma kada kuri’ar rashin amincewa da Dalhatu bisa sakamakon farko da Kwamitin Da’a da Halayya na kungiyar ya gabatar.

Ya bayyana cewa dakatarwar ba hukunci ba ne, illa don tabbatar da gudanar da bincike cikin gaskiya ba tare da cikas ba kan zarge-zargen da ke cikin karar da aka shigar kan shugaban kwamitin amintattun.

“NEC ta amince da dakatar da shugaban kwamitin amintattu tare da umartar gudanar da binciken kudi na gaggawa kan dukkan kudaden ACF, ba kawai kudin gidauniya ba.

“Wannan don tabbatar da gaskiya da kuma dawo da duk wani kudi da ba a yi amfani da shi yadda ya kamata ba bisa kundin tsarin kungiyar,” in ji Baba.

Ya kara da cewa kwamitin ya samu wujjar da ke nuna rashin gaskiya wajen harkokin kudi da kuma cin zarafin tsarin gudanarwa, inda ya bayyana cewa shugaban kwamitin bai amsa tambayoyin da aka yi masa ba ko kuma ya bayyana a gaban kwamitin binciken.

Baba ya ce NEC ta sake tabbatar da cewa babu rikicin shugabanci a kungiyar, tana mai bayyana abubuwan da ke faruwa a baya-bayan nan a matsayin yunkurin fassara da kwace ikon kungiyar ba daidai ba.

Ya bayyana cewa wakilan jihohi 18 na Arewa da Babban Birnin Tarayya ne suka halarci taron, wanda aka sauya wurin gudanarwa bayan jami’an tsaro sun rufe sakatariyar ACF.

A cewarsa, kungiyar ta soki toshe hedkwatarta da jami’an ‘yan sandan Najeriya suka yi, inda ta bayyana shi a matsayin abin da ba wajaba ba.

Baba ya ce kungiyar za ta ci gaba da jajircewa wajen kare mutuncinta da tabbatar da gaskiya a harkokinta.

Haka kuma, Shugaban Kwamitin Da’a da Halayya na ACF, Farfesa Nuhu Jamo, ya ce kwamitin ya yi aiki ne bisa karar da ke zargin shugaban kwamitin amintattun da mummunan hali.

Jamo ya ce kwamitin ya ba Dalhatu sa’o’i 48 ya amsa zarge-zargen, amma bai yi ba, lamarin da ya sa kwamitin ya ci gaba da aiki bisa shaidar da ke hannunsa.

Ya bayyaa cewa sakamakon binciken ya nuna cin zarafin kundin tsarin ACF, ciki har da shiga harkokin gudanarwa, shiga harkokin kudi ba daidai ba, da kuma hada wadanda ba mambobi ba a yanke shawara.

“Kwamitin ya kuma bayyana bayyanannun cin zarafin tanade-tanaden kundin tsarin da ke jagorantar gudanarwar kungiyar.

“Musamman shigar shugaban kwamitin ckin harkokin kudi da na gudanarwa ya haifar da damuwa mai tsanani,” in ji shi.

Jamo ya kara da cewa shawarar gudanar da binciken kudi zai tabbatar da bin tsari, gaskiya da kuma dawo da duk wani kudi da aka yi amfani da shi ba daidai ba. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here