Kungiyar Gwamnonin PDP a halin yanzu tana wani taro a Jos, babban birnin jihar Filato, inda suka jaddada aniyarsu ta mayar da jam’iyyarsu da dawo da fatawar ‘yan Najeriya.
Mai masaukin baki kuma Gwamnan Jihar Filato, Barr. Caleb Mutfwang, ya tabbatar wa magoya bayan jam’iyyar PDP cewa takwarorinsa da sauran masu ruwa da tsaki sun dukufa wajen sake yin dabarun daidaita jam’iyyar domin samun shugabanci na gari a Najeriya.
Gwamna Mutfwang ya bayyana hakan ne a ranar Juma’ar da ta gabata a yayin wani taro da aka gudanar a dakin taro na Banquet Hall da ke gidan gwamnati a garin Jos, inda ya karbi bakuncin kungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP domin gudanar da wani muhimmin taro.
Ya yi godiya ga gwamnonin da sauran amintattun jam’iyyar, wadanda suka yi tattaki daga fadin kasar nan zuwa ‘Gidan Zaman Lafiya da Yawon shakatawa’ domin tallafa wa taron. Ya kuma jaddada muhimmancin taron wajen tsara hanyoyin da jam’iyyar PDP za ta bi don dawo da martabar ta a matsayin jam’iyyar da ‘yan Najeriya ke so.