Majalisar dattawa ta amince da dokar hukunta masu lalata da ɗalibai

Senate
Senate

Majalisar dattijan Najeriya mai barin gado ta amince da ƙudirin dokar da zai haramta tare da hukunta duk malamin da aka samu da laifin cin zarafi ko lalata da ɗalibai a kwalejoji da jami’o’i a ƙasar.

Tun a shekarar 2020 Majalisar Dattawa ta amince da ƙudirin mai taken The Prevention, Prohibition and Redressal of Sexual Harassment in Tertiary Educational Institutions Bill amma ƙunshe da tanade-tanade daban.

Shugaban kwamatin Majalisar Dattawa kan harkokin shari’a, Sanata Opeyemi Bamidele, ya ce taron gamayyar ‘yan majalisar ya haɗe kan tanade-tanaden biyu kafin ya gabatar da rahotonsa a zauren Majalisar ranar Laraba.

Cikin tanadin dokar, akwai matakan daƙile yunƙurin aikata lalata da kuma cin zarafi na jinsi a dukkan matakin karatu na gaba da firamare a Najeriya.

Mataki na gaba shi ne miƙa kundin dokar ga Shugaba Bola Tinubu don ya saka mata hannu kafin ta zama doka a ƙasa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here