NAHCON Ta Sanya Wa Alhazan Najeriya Sabuwar Doka Kan Zaman Da Suke a Madina

Mecca New
Mecca New

Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON), ta sanar da wani tsari da za a buƙaci Alhazan Najeriya da ke Madina da su tafi zuwa Makkah bayan kwanaki biyar da isarsu birnin domin gudanar da aikin hajji.

Mataimakin daraktan yaɗa labarai na hukumar ta NAHCON, Mousa Ubandawaki, a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, ya ce dokar dai za ta fara aiki ne daga ranar Laraba da ta gabata.

Matakin dai na zuwa ne biyo bayan korafe-korafen cunkoson Alhazan Najeriya da ake samu a birnin na Madina daga mahukuntan Saudiyya.

Ubandawaki ya bayyana cewa, a baya hukumar na bai wa Alhazan Najeriya damar zuwa Madina dari bisa dari a matakin farko ko kuma kafin hawan Arafat.

Sai dai Ubandawaki ya ce an ɗauki wannan matakin ne don kaucewa takunkumin da akan iya sanyawa Najeriya, idan aka ci gaba da samun cunkoso a Madina. Ya ƙara da cewa sai da aka yi doguwar tattaunawa da kuma yin nazari kafin yanke hukuncin, musamman ma duba da yadda Alhazan Najeriya suka saba zama a Markaz na tsawon lokaci.

Ya bayyana cewa manufar wannan mataki shi ne, don a kaucewa hukunci da ka iya biyo baya kan kawo mahajjata da yawa zuwa Madina fiye da yawan masaukin da za a iya basu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here