Sarkin Bichin jihar Kano, Alhaji Nasir Ado Bayero ya yi kira ga masu kudi da kungiyoyi da su dinga taimakawa masu bukata ta musamman da kuma talakawa.
Jaridar Solacebase ta rawaitu cewa sarkin ya yi wannan kiran ne yayin kaddamar da wasu baburan guragu wadan da kungiyar youths for Better Nigeria tare da hadin gwaiwar babban daraktan hukumar tace fina finai ta kasa, suka bawa masarautar Bichi.
Ya yin bayar da baburan, sarkin Bichin ya jayo wasu ayoyi daga cikin al-qur’ani mai girma wadanda suke nuna mahimmancin taimakawa mabukata.
Ya kuma yabawa wadanda suka bada gudunmawar tare da cewa sun bayar da taimakon a lokacin da ake bukatar sa, ya kara da cewa baburan zasu taimaka matuka wajan ragewa wahalhalun da masu bukata ta musamman suke fuskanata wajan gudanar da al’amuran su na yau da kullum.
Ya kuma yi alkawarin cewa masarautar zata sa ido wajan ganin wadan da akabawa babauran basu sayar da su ba.
Ya yin da yake mika mashinan zuwa ga sarkin, shugaban kungiyar committed youths for Better Nigeria, Ambasada Ibrahim I. Ibrahim ya ce kungiyar tare da hkumar tace fina finai ta kasa sun yanke shawarar bada gudun mawar ne ga masarautar Bichi, bisa himma da sarkin ya ke da ita don ganin an ciyar da al-uma gaba.
Da yake magana a gurin taron, farfesa Isa Jibrin Diso na jam’ar Bayero Kano, wanda ya samu wakilcin Malam Ibrahim Abdulkarim ya yi kira ga masu bukata ta musamnan din da su dage wajan neman ilimi da kuma yin sana’o’i da zasu dogara da kansu.
Wadan da suka rabauta da baburan sun fito da kananan hukumumi 9 dake masarautar.













































