Sanata Rufai Hanga, wanda ke wakiltar Kano ta Tsakiya, ya gana da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Fadarsa da ke Abuja a ranar Lahadi. Wannan ganawar na iya kara zafafa zancen da ake yi na yiwuwar sauya shekarsa zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
SolaceBase ta ruwaito cewa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin ne ya bayyana ganawar a sahihin shafinsa na Facebook a ranar Lahadi.
Barau ya ce shi ne ya jagoranci Hanga da tsohon Sanata Kabiru Gaya, wanda ya taba wakiltar Kano ta Kudu, zuwa Fadar Gwamnati domin ganawa da Shugaban Kasa kuma Babban Kwamandan Askarawan Tarayyar Najeriya, Mai Girma Bola Ahmed Tinubu.
“Mintina kadan da suka wuce, na jagoranci Sanata Rufai Hanga na Kano ta Tsakiya da tsohon Sanata Kabiru Gaya zuwa Fadar Shugaban Kasa, Abuja, domin ganawa da Shugaban Kasa kuma Babban Kwamandan Askarawa, Mai Girma Bola Ahmed Tinubu,” in ji Barau.
Ya bayyana ganawar a matsayin mai amfani amma bai bayyana abin da suka tattauna ba.
Wannan ganawar ta zo ne a daidai lokacin da ake ta cece-kuce cewa Hanga na iya shiga jam’iyyar APC bayan ya yi wasu ganawa da manyan ‘yan jam’iyyar.
Haka kuma, Kabiru Gaya ya bar APC a lokacin zaben fidda gwanin jam’iyyar sannan ya koma NDC, inda nan ma bai samu tikitin takarar Sanata ba.
SolaceBase ta rawaito cewa a ranar 19 ga Yuli, Hanga ya yi ganawa ta musamman da Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda da Sanata Barau a gidansa dake Abuja.
A lokacin Barau ya ce ya yi farin cikin karbar Shugaban APC da Hanga, inda ya ce tattaunawar su ta mayar da hankali ne kan inganta hadin kai, ci gaba da bunqasa Kano ta Tsakiya, Jihar Kano da kasa baki daya.
Ganawar ta 19 ga Yuli ta zo ne ‘yan kwanaki bayan Hanga ya kuma yi ganawa ta musamman da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda hakan ma ya kara jefa mutane cikin tunanin matakinsa na gaba.
Wannan shi ne karo na biyu Hanga da Shugaban APC na Kasa suka yi ganawa cikin kankanin lokaci, bayan da Farfesa Yilwatda ya taba kai masa ziyara.
Wasu majiyoyi da suka san harkokin siyasa sun shaida wa SolaceBase cewa wadannan ganawa wani bangare ne na tattaunawa kan yiwuwar Hanga ya sauya sheka daga NDC zuwa APC.
Hanga na daga cikin ‘yan siyasa na farko da suka zauna tare da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso bayan Gwamna Yusuf ya sauya sheka zuwa APC.
Sai dai ganawar sa ta karshe da Shugaba Tinubu ta kara zafafa zargin cewa Sanatan Kano ta Tsakiya na kara kusantar shiga jam’iyyar APC mai mulki.













































