Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) ya karyata ikirarin da Kamfanin rarraba wutar Lantarki na Kano (KEDCO) ya yi cewa an dawo da wutar lantarki a asibitin, yana gargadi cewa muhimman ayyukan lafiya suna cikin hadari.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa wannan na zuwa ne bayan sanarwar da KEDCO ta fitar a ranar Litinin inda ta bayyana cewa ta mayar da wuta a asibitin.
Sai dai a wata sanarwa da hukumar AKTH ta fitar a ranar Litinin, ta ce duk da ikirarin KEDCO, manyan gine-ginen asibitin ba su samu wutar lantarki ba.
Ta bayyana cewa muhimman sassa na lafiya kamar dakin kula da marasa lafiya masu bukatar kulawa ta musamman, dakin tiyata, dakin haihuwa da na jarirai suna aiki ne da janareto na gaggawa.
Labari mai alaƙa: KEDCO ya yi ƙarin bayani kan wutar lantarki a Asibitin AKTH, tare da musanta zarginsa da alhakin mutuwar mutane
“Ashe ba daidai ba ne cewa an dawo da wuta kuma an ware masu sadarwa, domin har yanzu gine-ginenmu ba su da wuta. Muhimman sassa suna ci gaba da dogaro da inji,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta kuma tabo rikicin biyan kudin wuta da KEDCO, inda ta ce rahotannin cikin gida sun nuna bashin ya kai Naira miliyan 800, sabanin ikirarin KEDCO na cewa bashin ya kai Naira 949,880,922.45.
AKTH ta dage cewa wannan adadi na cikin gida ya sha bamban da wanda kamfanin rarraba wutar ya wallafa.
Don kare lafiyar marasa lafiya a yayin wannan matsalar, asibitin ya dauki matakan gaggawa da suka hada da dakatar da ayyukan tiyata da ba na gaggawa ba, rage amfani da wuta a wuraren da ba na lafiya ba, da kuma rage ayyukan gudanarwa.
Hukumar ta jaddada cewa bai kamata rikicin kasuwanci ya zama barazana ga rayukan jama’a ba.
Ta ce: “Lafiyar marasa lafiya da ci gaba da kula da su shi ne fifikonmu. Duk wani rikicin kudi ko kasuwanci bai kamata ya zama sanadin rasa rayuka ba.”
AKTH ta kuma yi alkawarin ci gaba da bayyana gaskiya ga ma’aikata, marasa lafiya da jama’a yayin da ake ci gaba da kokarin daidaita bashin da ke tsakaninta da KEDCO.












































