Hukumar kashe gobara ta bayyana  abin da ya haifar da gobara a ma’aikatar kudi ta kasa

Finance
Finance

Hukumar kashe gobara ta tarayya ta bayyana cewa  hayaki da ya tashi a ma’aikatar kudi ta tarayya da ke tsakiyar babban birnin tarayya Abuja a safiyar Larabar, ya faru ne sakamakon tartsatsin batir inverter.

Jami’in Hulda da Jama’a na hukumar, Mista Paul Abraham, ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN.

“Ga masu kashe gobara, za a iya samun hayaki ba tare da wuta ba, amma sauran al’umma, duk inda aka ga hayaki to gobara ce,” in ji Abraham.

Ya ce a lokacin da hukumar ta samu rahoton barkewar gobarar, ta tura wata tawaga zuwa ma’aikatar domin shawo kan gobarar.

“Mun samu kiran ne da misalin karfe 7 na safe, nan take muka tura mutanenmu daga tashoshi uku – Garki, Sakatariyar Tarayya da Wuse.

“An shawo kan lamarin gaba daya kuma bai dagula kasuwancin ranar ba,” in ji shi.

Hakazalika, mai magana da yawun ma’aikatar kudi, kasafin kudi da tsare-tsare ta kasa, Mista Olajide Oshundun, ya kuma tabbatar da cewa dakin batirin ma’aikatar ne kadai abin ya shafa.

Oshundun ya shaidawa manema labarai a ma’aikatar cewa gobarar ta taso ne daga wani baturi da ya fashe wanda ya shafi wasu batura 16.

“Batun dakin baturi da ke karkashin ma’aikatar ne kadai abin ya shafa; gobarar bata shafi wani bangare na ma’aikatar ba

Oshundu ya ce, “An kara kararrawa mai mahimmanci kuma an shawo kan gobarar a cikin kimanin mintuna 20 bayan haka,” in ji Oshundu.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here