Shugaban Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON), Ambasada Ismail Yusuf, ya mika sakon ta’aziyya ga iyalin Malama Aishatu Muhammadu, maniyyaciya daga Jihar Adamawa, wadda ta rasu a ranar 9 ga Mayu.
Sanarwar da NAHCON ta fitar a ranar Lahadi ta ce matar mai shekaru 73 ta fuskanci bugun zuciya a hanyarta daga Jeddah zuwa birnin Madinah.
Sanarwar ta cewa Yusuf ya mika ta’aziyyar ne a wata tattaunawar waya da fan marigayiyar, Umaru Jauro Koko.
“Ya kuma yi addu’ar Allah ya ba iyalin hakurin jure wannan rashi da ba za a iya mayewa ba.
“Ya tabbatar wa iyalin goyon bayan gwamnati wajen tabbatar dawo da kayan marigayiyar cikin aminci, ciki har da BTA da takardar shaidar mutuwa, ta hannun Hukumar Jin Dadin Alhazan Jihar Adamawa,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa marigayiyar ta bar ‘ya’ya da jikoki da dama, daga cikin ‘ya’yanta akwai Abdullahi Bello, Babban Jami’in Rundunar Tsaro da Kare Kadarori ta Kasa (NSCDC) a Karamar Hukumar Ganye. (NAN)











































