Kano: Mun amince za mu goyi bayan a sake zaɓenka a 2027 – Ganduje ya tabbatar wa Abba

WhatsApp Image 2026 01 26 at 19.29.21 750x430

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya tabbatar wa gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, cewa jam’iyyar ta amince da ba shi cikakken goyon baya domin sake tsayawa takarar gwamna a zaɓen shekarar 2027.

Ganduje ya yi wannan bayani ne a Kano yayin tarbar Gwamna Abba Kabir Yusuf bayan komawarsa jam’iyyar APC, inda ya bayyana dawowar a matsayin lamari mai tarihi da kuma alheri ga jam’iyyar da Jihar Kano baki ɗaya.

Ya bayyana cewa an tattauna da duk masu burin tsayawa takara a jam’iyyar, kuma sun amince su marawa Gwamna Yusuf baya domin ya samu wa’adi na biyu, lamarin da ya nuna haɗin kai da daidaito a cikin APC a Kano.

Karanta: Gwamnan Kano ya koma jam’iyyar APC a hukumance

Ganduje ya jaddada cewa Gwamna Yusuf ɗan siyasa ne mai ra’ayin cigaba, wanda salon shugabancinsa da halayyarsa suka dace da akidar APC, tare da bayyana cewa a tsarin jam’iyyar, duk gwamna mai ci shi ne jagoran jam’iyyar a jiharsa, don haka Yusuf ya zama jagoran APC a Kano.

Ya kuma tabbatar da cewa APC za ta ba Gwamna Yusuf cikakken adalci da goyon baya a cikin jam’iyyar, tare da bayyana kwarin gwiwar cewa jam’iyyar za ta samu nasarori masu yawa a zaɓuka masu zuwa, ciki har da zaɓen shugaban ƙasa a 2027.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, ya yi kira ga magoya bayan APC da su bai wa Gwamna Abba Kabir Yusuf cikakken goyon baya domin samun nasara.

Komawar gwamnan daga NNPP zuwa APC ta haifar da manyan sauye-sauyen siyasa a Kano, inda wasu zaɓaɓɓun jami’ai da mambobin jam’iyya suka biyo shi sauya sheƙar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here