Ana zargin Iran da ci gaba da kama ƴan jarida da masu fafutuka

FB IMG 16642805001478183
FB IMG 16642805001478183

Masu fafutukar kare ‘yancin dan’adam sun ce Iran na kara matsa kaimi wajen kama ‘yan jarida da ‘yan gwagwarmaya daidai lokacin da ake ci gaba zanga-zangar kin jinin gwamnati a fadin kasar.

Kwamitin Kare ‘Yan Jarida mai sansani a birnin Washington ya ce ‘yan jarida 20 aka daure tun bayan fara zanga-zangar a farkon wannan wata.

Zanga-zangar dai na da alaka da mutuwar Mahsa Amini, wadda ‘yan Hizba suka kama.

Masu fafutuka sun ce ta hanyar kama ‘yan jarida da iyakance musu shiga intanet da dandalin sada zumunta, hukumomin Iran na kokarin hana yada labaran zanga-zangar.

An kama ‘yan fafutuka ciki har da dan gwagwarmayar kare ‘yancin fadar albarkacin baki, Hossein Ronaghi da lauyoyinsa guda biyuwadanda aka tsare su tun ranar Asabar.

Dangin Hossein Ronaghi sun ce an lakada masa duka har kafarsa ta karye.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here