Masana kimiyya sun aika wani kumbon sararin samaniya da ya faɗa kan wani dutse mai nisa a ƙoƙarin ture shi daga kan hanyarsa ta sullubowa zuwa duniyar nan tamu.
Hukumar binciken sararin samaniyan Amurka Nasa ta bayyana aikin a matsayin gwajin harkar tsaro na farko a duniyarmu ta Az (Earth) domin kare wani dutsen yin karo da ita nan gaba.
A cewar wakiliyar BBC dutsen na asteroid da ake kira Dimorphis ya fara bayyana ne a matsayin hasken wuta sannan ya fara kumbura yayin da kumbon zuwa sama yake tunkarar sa.
Za dai a ɗauki tsawon makonni kafin masanan su iya gano ko an samu cikas a yadda dutsen yake zagaye duniya.













































