Rikincin PDP: Gwamna Ortom Ya Raba Gari Da Wike, Ya Ce Yana Tare Da Ayu 

Ortom 750x430 1
Ortom 750x430 1

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, a ranar Litnin, ya yi watsi da rahotannin cewa yana goyon bayan tsige Shugaban uwar jam’iyyar (PDP), Dr. Iyorchia Ayu. Ortom yace ba zai yiwu ya goyi bayan cire Ayu ba saboda shi ya tabbatar da zamanshi shugaban jam’iyyar.

Ortom ya jaddada goyon bayansa ga Ayu, wannan ya nuna barrantarsa da gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike.

Gwamnan ya bayyana hakan a martanin da yayi ga kungiyar Jemgbagh Development Association, dake zargin Ortom da hada kai da wasu wajen yiwa dan jiharsa zagon kasa.

A jawabin da sakataren yada labaransa, Nathaniel Ikyur, ya fitar a Abuja, Ortom yace kowa ya sani cewa su sukayi aiki tukuru wajen tabbatar da cewa Ayu ya zama shugaban PDP.

“Saboda haka, ba zai yiwu gwamna ya juya masa baya yace sai an cireshi ba,” a cewar jawabin.

Ya karyata zargin kungiyar Jemgbagh na cewa da hannun Ortom cikin yunkurin tsige Ayu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here