Tinubu ya amince da karin albashin jami’an Sojin Najeriya

Bola Tinubu signs 750x430 1

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da karin albashi daga kashi 30 zuwa 80 cikin dari ga jami’an Sojin Najeriya, inda kimanin jami’ai 250,000 ake sa ran za su amfana da sabon tsarin albashin.

A cewar sanarwar da Mai baiwa Shugaba shawara na musamman kan Harkokin Yada Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Talata, karin albashin zai fara aiki ne daga 1 ga Satumba, 2026.

A karkashin sabon tsarin, jami’an da suka wuce matsayin colonel, ciki har da brigadier-general, major-general, lieutenant-general da general, za su samu karin albashi na kashi 30 bisa dari.

Jami’ai daga matsayin colonel har zuwa warrant officer za su samu karin kashi 50 bisa dari, yayin da jami’ai daga matsayin private har zuwa staff sergeant za su amfana da karin kashi 80 bisa dari.

Sabon tsarin albashin ana sa ran zai karawa kasafin kudin albashin jami’an Soji na shekara daga Naira biliyan 660 zuwa Naira biliyan 924.

Shugaba Tinubu ya ce wannan shawara na daga cikin kudurin gwamnatinsa na inganta walwalar jami’an soji da ke yaki da ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane da ta’addanci a fadin kasar.

“Namiji da mace da ke taimaka mana mu zauna lafiya a gidajenmu dole ne a goyi bayan su tare da nuna godiya a yayin da suke gudanar da aikin su na bautawa kasar mu,” in ji Shugaban.

Ya kara da cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da ba da fifiko ga walwalar sojoji tare da zamantar da tsarin Sojin Najeriya ta hanyar samar da makamai da kayan aiki na zamani da ake bukata domin gudanar da aikinsu yadda ya kamata.

“Gwamnatin mu na da imanin cewa ba za a iya samun girma a kasa ba tare da tsaro ba. Saboda haka muna tsaye tsayin daka wajen tattara dukkan karfin soji da na tsaro domin kawar da barazanar tsaro da kare rayuka da dukiyar dukkan ‘yan Najeriya,” in ji Tinubu.

Shugaban ya bukaci jami’an Soji su dauki karin albashin a matsayin nuni na yadda gwamnati ke godiya ga hidima da sadaukarwarsu.

“Ina rokon sojojin mu su dauki wannan alherin namu a matsayin nuni na yadda muke yaba hidimar da suke yi wa kasa. Tare za mu yi nasara kan abokan gaba da ke son rusa tsarin kasar mu,” in ji shi.

Wannan sanarwa ta zo ne a lokacin da Sojin Najeriya ke ci gaba da fuskantar kalubalen tsaro, ciki har da ta’addanci, ‘yan bindiga da garkuwa da mutane a sassa daban-daban na kasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here