Kotu ta bada sammacin kama tsohuwar ministar man fetur Diezani Alison Madueke

Diezani Alison Madueke
Diezani Alison Madueke

A ranar Litinin ne wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta bayar da sammacin kamo tsohuwar ministar albarkatun man fetur, Diezani Alison-Madueke, wadda ake kyautata zaton tana zaune a kasar Birtaniya.

Mai shari’a Bolaji Olajuwon ya amince da bukatar ne bayan lauyan Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati EFCC, Farouk Abdullah, ya gabatar da bukatar baka.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ya rawaito cewa kotun ta sanya ranar 3 ga watan Nuwamba, 2021 ga hukumar EFCC da ta bayar da rahoto kan kokarin da ta yi na mika Alison-Madueke ga kasar domin ta tsaya mata shari’a.

Amma a ranar da aka dage sauraron shari’ar, ba a ga Abdullah ko Alison-Madueke ba.

Daga nan sai mai shari’a Olajuwon ya sanya ranar 24 ga watan Janairu kan lamarin kuma ya dage ci gaba da sauraron karar.

NAN ta ruwaito cewa duk da dai tun farko mai shari’a Ijeoma Ojukwu ita ce mai shari’a a kan lamarin, an mayar da shari’ar zuwa ga mai shari’a Olajuwon, bayan da aka mika Ojukwu zuwa sashin Calabar na kotun.

Dangane da gazawar tsohuwar ministar wajen karrama sammacin, hukumar EFCC ta bakin lauyanta, Abdullah, ta bukaci mai shari’a Ojukwu da ya bayar da sammacin kama ta, yana mai cewa tsarin mika mata ya ci tura sakamakon rashin samun takardar. na kama.

Alkalin wanda ya ki amincewa da bukatar, ya umurci lauyan da ya shigar da kara a kan hakan da wasu shaidun da suka samu daga ofishin babban mai shigar da kara na kasa (AGF), sannan ya dage ci gaba da sauraron karar da kuma yiwuwar gurfanar da wanda ake kara (Alison-Madueke).

Sai dai kuma a ranar litinin da aka kira al’amarin, Abdullah yana gaban kotu.

Ya shaida wa kotun cewa duk kokarin da hukumar ta yi na ganin an mika tsohuwar ministan a lokacin da lamarin ke gaban Ojukwu bai yi nasara ba.

Daga nan sai mai shari’a Olajuwon ya amince da bukatar sannan ya dage ci gaba da sauraron karar har sai an kama wanda ake kara (Alison-Madueke) aka gabatar da ita a gaban kotu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here