Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB ta sanar da ranar da za a fara rijistar jarrabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandire ta 2022 da kuma jarrabawar shiga kai tsaye, DE.
Daraktan hulda da jama’a na hukumar ta JAMB, Dr Fabian Benjamin ne ya bayyana hakan a ranar Litinin, a cikin sanarwar da hukumar ke fitarwa mako-mako.
Solacebase ta ba da rahoton cewa bisa ga sanarwar, aikin rajistar zai fara ne a cikin Fabrairu 2022.
Hukumar ta ce za a fara rajistar UTME/DE daga ranar 12 ga Fabrairu, 2022, kuma za ta kare a ranar 19 ga Maris.