Mai horas da Super Eagles na rikon kwarya Eguavoen ya ajiye aikinsa

EGUAVOEN
EGUAVOEN

Austin Eguavoen ya bar mukaminsa na kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles na rikon kwarya bayan da aka fitar da kungiyar daga gasar cin kofin nahiyar Afirka ranar Lahadi.

Bayan kammala wasannin rukuni-rukuni, kungiyar ta kasa samun nasara a kan Tunisia, wanda hakan ne ya kawo karshen aikin Eguavoen wanda ya yi fatan ci gaba da aikin na dindindin.

Duk da cewa hukumar kwallon kafa ta Najeriya ta shiga tattaunawa da wani koci dan kasar Portugal Jose Peseiro, amma akwai wasu shawarwarin da ke cewa Eguavoen na da damar ci gaba da aikin idan har zai iya lashe gasar AFCON a karo na hudu.

A wani taron manema labarai bayan kammala wasan, Eguavoen ya ce ya yanke shawarar komawa matsayinsa na Daraktan fasaha na NFF.

“Abin da zai biyo baya shi ne; Ni ne kocin rikon kwarya kuma daraktan fasaha na NFF, zan koma kan mukamina kuma in ba wa Hukumar damar yanke shawara kan hanyar da za a bi.” Eguavoen ya ce.

Yanzu dai hankali zai karkata ne ga wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da Ghana da aka kayyade a watan Maris.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here