Matsayin FIFA: Najeriya ta kare shekarar 2025 a matsayin ta 38 a Duniya

Super Eagles sabo 750x430

Sabbin jerin matsayi na hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA da aka fitar ranar Litinin, sun nuna cewa tawagar kwallon kafa ta Najeriya za ta kammala shekarar 2025 a matsayi na 38 a duniya.

Matsayin Najeriya bai canza ba idan aka kwatanta da jerin da aka fitar a watan Nuwamba, bayan da tawagar ta samu ci gaba da hawa matakai uku daga matsayi na 41 a baya.

A matakin Afirka, tawagar kwallon kafa ta Najeriya ta ci gaba da riƙe matsayi na shida, lamarin da ya nuna daidaiton matsayinta a nahiyar duk da canje-canjen da aka samu a duniya.

Gaba ɗaya, shekarar 2025 ta kasance mai gauraye ga Najeriya, amma tawagar ta kammala shekarar a matsayi 6 sama da inda ta fara a farkon shekarar, inda ta shiga shekarar ne a matsayi na 44.

Jerin farko na shekarar da aka fitar a watan Afrilu ya ɗaga Najeriya zuwa matsayi na 43, kafin daga bisani ta koma matsayi na 44 a watan Yuli da na 45 a watan Satumba.

Watan Oktoba ya kawo sauyi mai kyau, inda Najeriya ta haura zuwa matsayi na 41 bayan samun lambar azurfa a gasar cin kofin nahiyar Afirka AFCON, abin da ya zama mafi girman ci gabanta tun farkon shekarar 2024.

A matakin Afirka, ƙasar Maroko ce ke jagoranci da matsayi na 11 a duniya, sai Senegal a matsayi na 19, yayin da Aljeriya ta haura zuwa matsayi na 34, Masar kuma ta koma matsayi na 35, inda ta zama ta biyar a Afirka.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here