Gudun wuce sa’a da Motar tirela ke yi a hanyar Gombe ta yi sanadiyar mutuwar mutane tara – FRSC

FRSC FRSC

Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa FRSC ta tabbatar da mutuwar mutane tara sakamakon wani mummunan hatsarin hanya da ya faru a titin Kaltungo–Cham, a ƙauyen Kaluwa da ke ƙaramar hukumar Kaltungo a jihar Gombe.

Kwamandan sashen FRSC na jihar Gombe, Samson Kaura, ya tabbatar da aukuwar hatsarin a hirarsa da kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ranar Litinin.

Ya ce, mutane 18 ne hadarin ya rutsa da su, inda mutane biyar suka jikkata da raunuka mabambanta, yayin da wasu huɗu suka tsira ba tare da samun rauni ba a hatsarin.

Mutanen da suka jikkata an garzaya da su zuwa babban asibitin Kaltungo domin samun kulawar lafiya, yayin da aka ajiye gawarwakin waɗanda suka rasu a ɗakin ajiye gawarwaki na asibitin.

Binciken farko da FRSC ta gudanar ya nuna cewa hatsarin ya faru ne sakamakon kwacewar iko na abin hawa, wanda gudu mai yawa da matsalar birki suka haddasa.

Rahoton ya nuna cewa hatsarin ya shafi motar tirela da mota Sharon, inda tirelar da ke gangarowa kan hanya ta buge motar daga baya, lamarin da ya sa motar ta kife.

RSC ta sake jaddada kira ga direbobi da su guji gudu mai yawa tare da duba motocinsu kafin tafiya, musamman a wannan lokaci na bukukuwan ƙarshen shekara.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here