Donald Trump ya janye jakadan Amurka a Najeriya da wasu 29

Richard Miller 750x430

Shugaban ƙasar Amurka Donald Trump ya janye jakadan Amurka a Najeriya, Richard M. Mills Jr., tare da wasu manyan jami’an diflomasiyya 29 daga muƙaman jakadu da muƙaman ofisoshin jakadanci a faɗin duniya.

Richard M. Mills Jr., wanda aka naɗa a matsayin jakada a shekarar 2024, yana cikin jakadu 13 da ke aiki a ƙasashen Afirka da wannan mataki ya shafa, inda masu ruwa da tsaki a Washington suka bayyana cewa manufar matakin ita ce sake fasalin manufofin harkokin waje na Amurka bisa tsarin America First na Trump.

Kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya rawaito cewa jami’an da abin ya shafa, da dama daga cikinsu an naɗa su ne a lokacin gwamnatin Joe Biden amma suka ci gaba da aiki a farkon watannin mulkin Trump, an sanar da su a makon da ya gabata cewa wa’adinsu zai ƙare a watan Janairu na shekarar 2026.

Rahoton ya bayyana cewa jakadu suna aiki ne bisa yardar shugaban ƙasa, kodayake a al’ada suna ci gaba da zama a muƙamansu na tsawon shekaru uku zuwa huɗu kafin sauyawa.

Jami’an da abin ya shafa, waɗanda suka nemi a sakaya sunansu, sun bayyana cewa ba a kore su daga aikin harkokin waje ba, sai dai za a mayar da su Washington domin ɗaukar wasu muƙamai idan sun zaɓi ci gaba da aiki.

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta sanar da jaridar Guardian ta Birtaniya cewa an sanar da shugabannin ofisoshin jakadanci tun a makon da ya gabata cewa wa’adinsu zai ƙare a watan Janairu, inda ma’aikatar ta jaddada cewa jakada wakili ne na musamman na shugaban ƙasa, kuma yana da haƙƙin zaɓar mutanen da za su aiwatar da manufofinsa.

Nahiyar Afirka ce ta fi fuskantar wannan sauyi, inda aka janye jakadu daga ƙasashe 13 da suka haɗa da Burundi, Kamaru, Cape Verde, Gabon, Côte d’Ivoire, Madagascar, Mauritius, Niger, Najeriya, Rwanda, Senegal, Somalia da Uganda, lamarin da ya zama ɗaya daga cikin manyan sauye-sauyen diflomasiyya a zangon mulki na biyu na Donald Trump.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here