Kungiyar manyan ma’aikatan jami’o’in Najeriya SSANU da kungiyar ma’aikatan jami’o’i NASU sun dakatar da yajin aikin da suka tafi na watan ni.
Mohammed Haruna Ibrahim, shugaban SSANU ya ce sun dakatar da yajin aikin na kawai kwana 30 don bawa gwamnati lokaci ta cika musu alkawurran da suka dauka.
Kwamared Ibrahim ya ce za su koma yajin aikin idan har wa’adin din ya cika kuma gwamnatin tarayyar bata cika dukkan alkawurran da ta daukar musu ba
Ana sa ran janyewar zai fara aiki ne daga ranar Laraba na mako mai zuwa.













































