Gwamnatin Kaduna a karyata jita-jitar cewa madatsar ruwa ta Kangimi na shirin rushewa

Kangimi dam in Kaduna

Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi watsi da rahotannin da ke ikirarin cewa madatsar ruwa ta Kangimi da ke Karamar Hukumar Igabi na daf da rushewa.

Idan za ku iya tunawa, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA) ce ta ja hankali kan fargaba game da rahotannin lalacewar tsari da kuma tsagewar da ake gani a madatsar ruwan ta Kangimi da ke Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna.

Hukumar ta yi gargadin cewa duk wani babban tsaiko ko rushewa na madatsar ruwan zai iya jifa al’ummomin da ke zaune a kusa da kogin a jihohin Kaduna, Neja da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja cikin gagarumin hadari.

Babban Daraktan NSEMA, Abdullahi Arah, ya bayyana damuwarsa a cikin wata sanarwa, inda ya bukaci a gudanar da bincike na gaggawa a madatsar ruwan tare da daukar matakan kariya nan take.

Sai dai, Babban Sakatare a Ma’aikatar Ayyukan Jama’a da Gidaje ta Jihar Kaduna, Alh. Ashiru Abdu Na Abdu, ya fayyace lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.

Na Abdu ya ce gwamnati ta yaba kan damuwar da jama’a suka nuna biyo bayan gargadin ambaliyar ruwa da Hukumar Kula da Yanayi ta Kasa (NiMet) ta fitar kwanan nan, wanda ya hada da Jihar Kaduna cikin jihohi 10.

Haka zalika, ya bukaci mazauna yankin da su dogara da sahihan bayanai domin kauce wa fargabar da ba ta da muhimmanci game da yanayin madatsar ruwan.

A cewarsa, hotunan da ke yawo a kafofin sada zumunta suna da alaka ne da matsalolin tsari da aka fara lura da su a madatsar ruwa ta Kangimi tun a shekarar 2015 da 2016.
Ya ce wadancan matsalolin sun samo asali ne sakamakon tsufan madatsar ruwan da kuma matsin lamba daga kwararan ruwan sama da aka yi a wancan lokacin.

Babban sakataren ya ce nan take Ma’aikatar Ayyukan Jama’a da Gidaje ta Jihar Kaduna ta gudanar da ayyukan gyara na gaggawa domin daidaita madatsar ruwan.

Na Abdu ya ce Hukumar NEMA tare da hadin gwiwar Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna (SEMA) suna gudanar da taron fadakarwa ga al’umma.

Ya bukaci mazauna yankunan da ke kusa da madatsar ruwan da su kwantar da hankalinsu, su kasance masu sanya ido, sannan su kai rahoton duk wani abu da ba su gane ba ga hukumomin da ke kusa da su.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here