Majalisar wakilai a Najeriya za tayi bincike kan abinda ke tsakanin Matatar Man Dangote da Hukumar kula da Man Fetur ta Najeriya (NMDPRA).
Mataimakin mai magana da yawun majalisar wakilai, Philip Agbese, ne ya shaida hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja ranar Asabar.
NAN ta tabbatar da cewa binciken na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da matsalar karancin mai a fadin kasar da kuma zargin cewa man Dangote ba shi da inganci.
Agbese, ya ce binciken ya yi daidai da kudurin majalisar na kare dukkan kadarorin kasa da ababen more rayuwa na tattalin arziki daidai da na matatar man Dangote.
Karin labari: Da Dumi-Dumi: Sanata Ifeanyi Ubah ya rasu
Ya kara da cewa, “mun dade muna gani ta hanyar yin kamfen don bata sunan matatar man Dangote da kuma la’akari da mummunan tasirin da hakan ya haifar da firgici a kasar” in ji shi.
Yace abin takaici, abin da muka gani shi ne, NNPC da NMDPRA na taka rawar gani sosai a cikin wadannan makirce-makircen don bata sunan matatar, wanda kuma ba za’a amince da shi ba, kamar yadda NAN ta wallafa.