Man dizal din mu ya kai matsayin ayi  gogayya dashi a duniya, don haka bashi da wata matsala – Matatar Man Dangote

Dangote Refinery

Matatar man Dangote ta sake tabbatar da cewa man dizal dinta yana da inganci idan aka kwatanta shi da wanda ake shigo da shi daga kashen waje, kuma ta kara tabbar da cewa  matar ta cika dukan ka’idoji kafin ta fara aiki.

Wannan dai na zuwa ne bayan  kalaman da babban jami’in hukumar kula da harkokin man fetur ta kasa (Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority (NMDPRA), Farouk Ahmed ya yi a baya-bayan nan, cewa man dizal din matatar Dangote bashi da inganci, wanda ake shigowa daga kasashen waje ya fishi inganci.

Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa matatar tace babu daya daga cikin man dizal da ake shigowa da shi Najeriya da zai iya yin gogayya da na matatar Dangote ta fuskar inganci kuma duk wani kwararre da ke da niyyar gwada man kofa a bude take.

Babban jami’in kasuwanci na rukunin kamfanonin Dangote, Rabiu A. Umar ne ya bayyana haka ranar Juma’a a Kano a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai.

“Man dizal din mu bashi da wata matsala kamar yadda ake yadawa cewa mara kyau ne, kuma mun kalubalanci duk wani kwararare ko masani da yake son ya gada man mu, toh kofah a bude take.”

A cewarsa, “ ko a lokacin da shugabancin majalisar wakilai, Hon. Tajudeen Abbas ya ziyarci matatar a karshen makon da ya gabata, a kan hanyarsu ta zuwa matatar ya tsaya ya  sayo man dizal daga gidajen mai guda biyu, inda aka kwatanta da na matatar man Dangote; sun yi mamakin sakamakon ingancin samfuranmu.”

“Gwajin da aka gudanar a gabansu ya tabbatar da ingancin man dizal din namu kuma ya tabbatar da cewa dizal din mu na daya daga cikin mafi inganci a duniya” inji Umar.

“Muna samar da dizal mafi kyau a Najeriya. Amma Abin ban takaici ne wadanda ya kamata su taimake ka, ba basu yi ba, kasa kudinka ka gina matata, kuma kana fitar da mai mai inganci, amma anzo ana bata man da kake fitarwa, ana yi maka zagon kasa. wannan abu bai dadi ba.”

Har ila yau, dangane da batun cewa matatar man har yanzu ba ta da lasisi, Rabi’u Umar ya musanta zancen.

“matatar mu ta cika dukan ka’idoji, kuma muna da lasisi, takardu da hujjoji ba sa  karya, mun bi dukkan hanyoyin da suka dace kafin matatar mu ta fara aiki.”

Ya bayyana matatar Dangote a matsayin abin alfaharin Najeriya da Afirka wanda bai kamata a barta ta mutu ba

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here