Abdul Samad Rabiu ya zarce Johann Rupert, ya zama mutum na biyu mafi arziki a Afirka da dukiya da ta kai dala biliyan 18.6

Abdul Samad Rabiu

Mamallaki kuma shugaban BUA Group, Abdul Samad Rabiu, ya zarce Johann Rupert, attajirin dan kasuwa dan Afirka ta Kudu , ya zama mutum na biyu mafi arziki a Afirka.

Ci gaban Rabiu ya zo ne bayan ya samu karin arziki mafi yawa a duniya baki daya, inji Bloomberg Billionaires Index (BBI).

Dukiyar Rabiu ta zarta zuwa dala biliyan 18.6, wanda ya sanya shi a matsayi na 138 a jerin masu arzikin duniya, kuma ya samu karin dala biliyan 8.47 tun daga farkon shekara.

Rahoton ya ce wannan karin arziki na bazata ya biyo bayan habakar da kamfanoninsa na masana’antu sika samu.

A baya an kiyasta dukiyar Rabiu da kusan dala biliyan 15.9, wanda ke nuna saurin ci gaban da ya samu a watannin baya-bayan nan.

Bisa ga jerin, dukiyar Johann Rupert ta fadi zuwa dala biliyan 17.9 bayan ya yi asar kusan dala biliyan 1.76 a bana, lamarin da ya sa dan kasuwan Afirka ta Kudu ya koma matsayi na 153 a duniya.

Bayanai daga BBI sun nuna Rabiu shi ne dan kasuwa dan Afirka da ya fi kowa samun ci gaba a shekarar 2026, sakamakon riba a kasuwancinsa na siminti, abinci, da masana’antu.

Sakamakon sabon jerin ya bar Rabiu a baya Aliko Dangote a tsakanin ‘yan kasuwan Afirka masu attajirai.

Kididdigar bayanai ta nuna Dangote ya rike matsayinsa a matsayin mutum mafi arziki a Afirka, da dukiyar dala biliyan 34.4, wanda ya sanya shi a matsayi na 66 a duniya bayan ya kara kusan dala biliyan 4.38 a dukiyarsa a bana.

OTEDOLA DA MIKE ADENUGA BA SU CIGABA DA ZAMA A JERIN BA

Ya zuwa ranar 7 ga Mayu, jerin na Bloomberg bai hada da wani dan Najeriya ba a jerin masu arziki na duniya.

Sakamakon sabon jerin ya nuna Mike Adenuga, wanda ya kafa Globacom, da dukiyarsa ta kai dala biliyan 6.5, da Femi Otedola, shugaban Geregu Power Plc (dala biliyan 1.3), ba su cikin jerin mutane 500 mafi arziki a duniya.

Otedola ya sayar da mafi yawan hannun jarinsa a Geregu Power Plc kan Naira 1.088 tiriliyan a yarjejeniyar da kungiyar bankuna karkashin Zenith Bank Plc suka dauki nauyi a shekarar 2025.

A watan Maris, Forbes ta ce Rabiu shi ne dan kasuwa dan Afirka da ya fi kowa samun riba bayan dukiyarsa ta karu da dala biliyan 6.1 a shekarar da ta gabata.

A cewar mujallar, dukiyar Rabiu ta karu da kusan kashi 120 (dala biliyan 6.10) zuwa dala biliyan 11.2, wanda ya sanya shi a matsayi na uku a jerin masu arziki a nahiyar – daga matsayi na shida da ya kasance a baya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here