Kwamitin yaki da miyagun kwayoyi na Kano ya kama tsohon shugaban Karamar Hukuma kan zargin sayar da miyagun kwayoyi

IMG 20260802 WA0487 750x430 (1)

Kwamitin Hadin Gwiwa na Jihar Kano dake Yaki da Miyagun Kwayoyi da sauran Laifuka masu alaka, ya kama tsohon Shugaban Karamar Hukumar Rogo bisa zargin shiga cikin sayarwa da kuma bai wa matasa alluran fentanyl ba bisa ka’ida ba.

Shugaban Kwamitin, Muhuyi Magaji Rimingado, ne ya bayyana hakan a cikin wata hira da wata kafar yada labarai a ranar Litinin, kamar yadda SolaceBase ta ruwaito.

Rimingado ya ce an kama wanda ake zargin ne bayan kwamitin ya gudanar da binciken sirri don tabbatar da zargin da ake yi masa na sayarwa da kuma bai wa matasa wannan abu.

Ya bayyana cewa binciken ya fara ne bayan sun kama wani matashi wanda aka ce hannunsa ya lalace sosai sakamakon alluran da aka masa.

“Mun kama wani a Kano da ke sayar da maguwar allura, kuma tsohon shugaban karamar hukuma ne. Muna zargin yana bai wa mutane wannan maganin dake cutar da su,” in ji Rimingado.

A cewarsa, matashin da aka kama ya bayyana tsohon shugaban karamar hukumar a matsayin wanda yake karba daga gare shi, sannan ya bayyana yadda suke yin ciniki.

Rimingado ya ce wanda ake zargin kan karbi kudi daga masu saya sannan ya ce su tafi su dawo, kafin ya kawo musu maganin da aka boye a cikin envelop, wani lokacin tare da sirinji.

Ya ce kwamitin daga bisani ya ba matashin kudi ya ce ya koma wurin wanda ake zargin, yayin da jami’ansu ke biye da shi suna lura da cinikin daga nesa.

“Da ya je can, ya ba mutumin kudin aka ce ya tafi ya dawo. Da ya dawo, wanda ake zargin ya riga ya saka maganin a envelop. Yayin da zai ba shi, jami’anmu suka shiga suka kama shi,” in ji shi.

Shugaban kwamitin ya ce da farko wanda ake zargin ya musanta sanin inda ya samo maganin, yana mai cewa wani ne yake kawo masa daga Kasuwar Sabon Gari.

Amma Rimingado ya ce kwamitin na da isassun shaidu, ciki har da maganin da aka same shi da shi, shaidar wanda aka cutar da kuma furucin wanda ake zargin.

“Na farko, muna da shaida saboda mun same shi da maganin. Na biyu, muna da wanda aka cutar. Na uku, shi kansa ya furta cewa yana saya, amma ba ta hanyar da ta dace ba. Don haka duk abin da muke son tabbatarwa an tabbatar,” in ji shi.

Rimingado ya ce matashin da ake zargin yana amfani da maganin ya bayyana cewa ya kashe sama da N2 miliyan wajen saya a tsawon shekaru biyu.
Ya bayyana hakan a matsayin abin damuwa da ke nuna yadda matsalar shan miyagun kwayoyi ta yi tsanani.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here