An ceto jarirai biyu da ambaliya ta yi awon gaba da su a Kongo

c9dd2a84 6134 4a59 9f50 bacff8d3cd8c
c9dd2a84 6134 4a59 9f50 bacff8d3cd8c

An ceto wasu jarirai biyu, bayan da aka tsince su a gaɓar kogin Kivu, kwanaki bayan wata mummunar ambaliya da ta haddasa hasarar rayuka ta afka wa gabashin jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo.

Mazauna wajen sun ce sun ga jariran suna motsi a cikin baraguzan gidanjen da ruwa ya tafi da su zuwa kogi.

“An ceto su da ransu. wannan abin al’ajabi ne, mun yi matuƙar mamaki,” kamar yadda Delphin Birimbi, wani shugaban al’umma a yankin Kalehe, ya shaida wa BBC.

Ya ce abin taƙaici iyayen waɗannan jarirai sun mutu.

“Muna kan tattaunawa da mutanen da za su taimaka wajen rainon jariran,” in ji ji.

A ranar Litinin ne aka kuɓutar da jariran a wurare daban-daban, ɗaya a ƙauyen Bushushu ɗaya kuma a ƙauyen Nyamukubi, wuraren da ambaliyar ta fi ƙamari a yankin Kalehe.

Mista Birimbi ya ce kawo yanzu kusan mutunen ƙauyen 2,255 ne ba a gani ba, tun bayan faruwar ambaliyar, kuma ana ci gaba da aikin ceto.

Fiye da mutum 400 ne suka mutu a makon da ya gabata sakamakon ambaliyar.

Mutanen yankin sun ce, mutum 200 ne aka kai cibiyoyin lafiyar yankin, sakamakon ambaliyar da ta lalata aƙalla gidaje 1,300 da makarantu da wuraren ibada da ababen more rayuwa masu yawa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here