Ana ci gaba da kada kuri’a a babban zaben kasar Bangladesh wanda ake kyautata zaton shugabar kasar mai ci Sheikh Hasina za ta lashe.
An tsaurara matakan tsaro, inda aka jibge jami’an soji da ‘yan sanda a sassa daban-daban na kasar, sakamakon yawaitar ayyukan zagon kasa da aka gudanar a yayin da ake shirye-shiryen zaben.
Karanta wannan: Shugaba Felix Tshisekedi ya sake lashe zaben kasar Congo
Jam’iyyar Awami mai mulki ta zargi ‘yan adawa da kaddamar da “ayyukan ta’addanci.” Amma Babbar jam’iyyar adawa ta BNP wadda ke jagorantar kaurace wa zaben tace bata da hannu a tashin hankalin.
Zaben ka iya sharewa Sheikh Hasina hanya wajen sake darewa kan kujerarta a karo na biyar bayan da babbar jam’iyyar adawa ta kaurace wa zaben.