Kano: Kotu ta janye umarnin kama wani jami’in hukumar hana fasa kauri

Kotu
Kotu

Wata kotun shari’ar Musulunci a Jihar Kano ta janye umarnin da ta bayar na kama wani jami’in Hukumar hana fasa-kauri, Yusuf Ismail Mai Biscuit, da ta bayar a ranar Alhamis.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa a ranar Alhamis ne kotun karakshin jagorancin Garba Hamza Malafa, ta bada umarnin kama Yusuf Ismail, wanda ake kara bisa hujjar cewa bai halacci kotun ba kuma bai sa wani ya wakilce shi ba.

Karanta wannan: Kotun Shari’ar Musulunci A Kano Ta Daure Lauyan Bogi Watanni 15 A Gidan Kaso 

Sai dai a wani umarni da ta bayar ranar Juma’a, babbar kotun shari’a, ta ce an janye umarnin na farko ba tare da bata lokaci ba.

Kotun ta ce janyewar ya biyo bayan bayanin lauyan da ke kare wanda ake kara, Barista Sani Idris, ya yi, wanda ya tabbatar da cewa wanda yake karewa yana kotun duk da yake ba’a kai masa da sammaci ba.

Karanta wannan: Kotun Daukaka Kara Ta Kori Kakakin Majalisar Nasarawa

Da yake magana da jaridar solacebase a ranar Juma’a, Barista Sani Idris, ya ce an yi wata balulluba ne lokacin da ya je kotun domin ya wakilci wanda yake karewa a kan lamarin yayin da shi kuma alkalin ke gudanar da shari’ar a ofishin sa.

Kotun ta sanya ranar 8 ga watan Janairu domin sauraron karar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here