Kotun Shari’ar Musulunci A Kano Ta Daure Lauyan Bogi Watanni 15 A Gidan Kaso 

Court Gavel
Court Gavel

An gurfanar da wani lauyan bogi mai suna Zaharaddin Sani Maidoki a gaban kotun shari’ar Musulunci bisa zargin yaudara da cin amana. Kotun da ke zamanta a karamar hukumar Kiru da ke jihar Kano ta daure wanda ake zargin watanni 15 a gidan kaso.

Wanda ake zargin wanda dan asalin jihar Kaduna ne ya bayyana kansa a matsayin lauya da niyyar kare wasu mutane a gaban kotu.

Zaharaddin ya amsa dukkan tuhume-tuhumen da ake kararsa akai wanda ya hada da bayyana kansa a matsayin dan jarida daga jihar Kaduna. Alkalin kotun, Abdulmuminu Nuhu ya daure wanda ake zargin watanni 15 a gidan gyaran hali, Aminiya ta tattaro.

Hukuncin da Alkalin kotun ya yanke bai ba da damar biyan kudin tara ba, amma zai biya N20,000. Yayin yanke hukuncin, Alkalin kotun ya daure matashin tare da yin amfani da dokokin shari’a ta jihar Kano karkashin sashe na 337.

Kotun har ila yau, ta tura sako zuwa Kungiyar Lauyoyi ta jihar Kaduna don tabbatar da ikirarin shi lauya ne, inda kungiyar ta ce ba ta san da zamanshi a kungiyar ba. Alkalin kotun ya shaida masa cewa yana da kwanaki 30 idan bai gamsu da hukuncin kotun ba zai iya daukaka kara.

Kotun ta kuma kwace dukkan wasu takardu da ke tare da shi da kuma shaidar katin aiki da yake ikirarin shi lauya ne kuma dan jarida.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here